Yayin da aka fara kada gangar siyasar zabe mai zuwa na 2019, kimanin 'ya'yan jam'iyyar APC mai mulki 14,000 suka sauya sheka ya zuwa jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Neja dake a Arewa ta tsakiyar Najeriya.
Mun samu dai cewa tuni jam'iyyar ta PDP a jihar ta kammala dukkan shirye-shiryen ta don shirya babban gangamin karbar su zuwa jam'iyyar.
Tsintsiya ta watse: 'Ya'yan jam'iyyar APC 14,000 sun sauya sheka zuwa PDP a Neja
Hausansi dai ta samu kuma cewa a kwanan baya ma akalla 1,500 ne suka canza sheka daga APC zuwa PDP din a karamar hukumar Kontagora yayin da kuma suka samu tarba da wani jigo na jam'iyyar PDP Yahaya Ability.
Mai karatu ma dai zai iya tuna cewa Shugaban jam'iyya mai mulki a Najeriya ta APC mai suna Cif John Odigie-Oyegun ya karbi tsohon gwamnan jihar Ebonyi da matar sa Josephine Elechi zuwa jam'iyyar ta su daga jam'iyyar PDP.
Labels: Labarai