- Naira ta rikewa Dalar Amurka kugu a wannan mako
- Darajar Nairar ba ta karye ba har zuwa jiya Talata
- Babban bankin kasar ne ke luguden Daloli a kasuwa
Mun samu labari daga Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN cewa an fara makon nan yayin da Naira ta ke nan da karfin a kasuwar canji. Jaridar Daily Trust ta kawo cikakken rahoto game da yanayin farashin kudin kasar.
Naira na nan da karfin ta a farkon makon yau
Naira na nan da karfin ta a farkon makon nan da aka shiga inda har yanzu ta ke nan N362.5 a kan kowace Dalar Amurka. Haka zalika kuma Fam Sterling na Kasar Birtaniya na kan N480. Euro kuma ya tashi a kan N430 a kasuwa.
A kasuwar masu sari na babban bankin Kasar na CBN kuwa ana saida Dalar ne kusan a kan N360 yayin da Sterling na Ingila da EURO na Turai su ka tashi a kan N365 da kuma N408 kamar yadda labari ya zo mana a yammacin jiya.
‘Yan kasuwa dai sun nuna farin cikin su kamar yadda dai mu ka ji, kuma ana sa rai cewa Naira za ta kara daraja a kasuwa yayin da babban bankin kasar na CBN ke cigaba da zazzago Daloli a kasuwa ko da dai wasu na sukar hakan.
Labels: Labarai