Sufeta Janar Idris yaki amsa tambayoyin da Majalisar Dattijai tayi masa

- Bayan zargin rashawa da ake masa, Sufeta Janar Idris ya bayyana a gaban kwamitin Majalisan Dattijai a ranar Laraba

- Sai dai Sufeta Janar Idris yaki amsa tambayoyin da kwamitin tayi masa bisa hujjar cewa kotu na gudanar da bincike akan zargin

- A cewarsa, ya bayyana gaban kwamitin majalisan ne domin yana daraja majalisar amma ba don ya amsa tambayoyi ba

Sufeta Janar na rundunar yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris ya fadawa kwamitin Majalisar Dattijai cewa ba zai amsa tambayoyin da suka masa ba a yayin da ya bayyana a gaban kwamitin domin maganar tana gaban kotu.

Sufeta Janar Idris ta bakin lauyan sa, Alex Iziyon yace ya amsa kiran kwamitin ne domin yana daraja su kuma shi mutum ne mai biyaya ga doka da oda. Ya kara da cewa duk wani sharhi da zaiyi yana iya kawo mishikila ga shari'ar da ake gudanarwa.

Sufeta Janar Idris yaki amsa tambayoyin da Majalisar Dattijai tayi masa

Majalisar ta bukaci Idris ya bayyana gaban ta ne bayan Sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya, Isah Misau ya zargin Sufetan da rashawa ta hanyar karban kudade daga wasu kamfanoni domin samar musu da tsaro ba tare da bin ka'ida ba.

Ciyamin din kwamitin Majalisar datawan, Francis Alimekhena yayi masa tambaya akan zargin da ake masa na karkatar da wani kaso daga kasafin kudin 2016 na rundunar yan sanda tunda wannan maganar bata kotu, amma daga baya Alimekhena yace kwamitin zata sake gayyatar Sufeta Janar din bayan sun duba takardun kasafin kudin.

Labels: