Sojojojin Najeriya sun fatattaki ‘Yan Boko Haram sun kuma ceto mutane da dama

- Sojojin Najeriya sun ceto jama’a da dama daga hannun Boko Haram

- Rundunar Sojojin Kasar sun kuma kama wani ‘Dan ta’adda a Yankin

- Yanzu haka ana cigaba da gudanar da bincike Inji Darektan Sojojin

Labari ya kai gare mu cewa har wa yau ana cigaba da karasawa da ‘Yan ta’addan da ke Yankin Borno kamar yadda Darektan yada labarai na gidan Sojin Brigdeiya Janar Sani Kukasheka Usman ya sanar.

Kadan daga cikin makaman da Sojoji su ka samu

Rundunar Sojin Najeriya na Bataliya ta 202 ta Operations LAFIYA DOLE sun yi nasarar kama wani ‘Dan Boko Haram inda su ka same shi dauke da makamai iri-iri. An samu damar karbe bindigogin AK-47 da dama da harasashi da adda da sauran su.

Sojojin sun samu wannan nasara ne da hadin gwiwar Rundunar Operation DEEP PUNCH 2 a Ranar Asabar din ta gabata. An kuma yi nasarar ceto wasu maza 3 da ma wasu mata 12 da yara har 15 daga hannun ‘Yan ta’addan na Boko Haram.

Sojojin Najeriya na cigaba da fatattakar ‘Yan ta’adda a a Garuruwan Jihar Borno da su ka hada da; Abusuriwa, Newchina, Bonzon, Usmanari, Goyayeri, Shitimari, Gashimari, Awaram da ma wasu Kauyuka a cikin Garin Bama da ke Jihar.

Labels: