Sojoji sun kai harin bazata ga yanta’addan Boko Haram dake shirin shiga dajin Sambisa, kalli abubuwan da suka samo

Rundunar soji sun kai hari bazata ga yan ta’addan Boko Haram a Borno
- Yan ta’addan na kokarin shiga dajin Sambisa
- Rundunar sun kuma samo wasu makamai da yan ta’addan ke amfani da shi
Rundunar bataliya 152, 21 briged na soji, a aikinta na Operation Lafiya dole a cigaba da ayyukan datsewa da sharan DEEP PUNCH 2 da kuma magance sauran yan ta’addan kungiyar Boko Haram dake zaune a wasu yankuna, sun kai wa yan ta’addan Boko Haram harin bazata a safiyar Juma’a, 3 ga watan Nowamba 2017, a hanyar Banki-Bula Yobe dake karamar hukumar Bama na jihar Borno.
Rundunar sun kai wa yan ta’addan farmaki inda suka kashe daya daga cikin su sannan suka karbe kekuna 4, kayan gyaran ababen hawa wanda ke taimaka wa ababen hawan yan ta’addan, kayayyakin sawa da kuma wayoyin kaya masu fashewa a harin bazatan.
A makamancin haka, dakarun 151 na rundunar sojin, 21 Briged, har ila yau ta kai harin bazata kan yan kungiyar Boko Haram wadanda suke niyyan ketara zuwa cikin jejin Sambisa da misalin karfe 7:40 na yamma a wannan rana, a hanyar BOCOST-Bama. Rundunar ta kau da wasu yan ta’addan sannan wassu suka tsere da rauni.
A cewar kakakin rundunar sojin, Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman, rundunar sun ceci ran wani yaro mai shekaru 6 sannan suka karbe kayayaki masu yawa wadanda suka hada da, kekuna 8, bargo, jarkoki na ruwa, kwanuka, spanners, adduna, riguna da tufafin aikin yan ta’addan Boko Haram. Yaron da aka ceto yana a asibiti inda ake bashi cikakken kulawa a asibitin rundunar soji.
Ga hotunan kamu da sukayi a kasa:
Rundunar soji ta kai harin bazata ga yan ta’addan Boko Haram, ta kau da mutun daya

Labels: