Siyasa: An sha alwashin ganin APC ta sha kashi a 2019

Wata Kungiyar Yarbawa ta ce PDP za ta karbi mulki a 2019

- Kungiyar tace sam Jam’iyyar APC ba za ta dawo mulki ba

- A cewar su dai Jam’iyyar APC ta ba ‘Yan Najeriya kunya

Mun samu labari cewa wata Kungiya a Jihar Ondo ta sha alwashin ganin Jam’iyyar APC ba ta kai labari a zabe mai zuwa ba.

Jam'iyyar APC a wajen yakin neman zabe

Wata kungiyar siyasa a Yankin Yarbawa mai suna Sunshine Integrity Vanguard ta zare takobi inda tace ko ana ha-maza-ha-mata APC ba za ta koma mulki ba a 2019. Kungiyar tace tun da APC ta karbi mulki abubuwa su kayi ta sukurkucewa a kasar.

Kungiyar ta bakin Shugaban ta Andrew Ogunsakin ke cewa Jam’iyyar APC ba za ta dawo mulki ba a zabe mai zuwa don kuwa makaryata ne kurum kuma sun ba mutanen Najeriya kunya. Ogunsakin yayi wannan jawabi ne a Garin Akure da ke Jihar Ondo.

Andrew Ogunsakin yake cewa bisa dukkan alamu a zabe mai zuwa sai fa an yi da gaske za a hana Jam’iyyar PDP komawa mulki a kasar kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Labels: