Shugaban Kasar Zimbabwe Mugabe yana cikin babbar matsala

Sojoji a Zimbabwe sun dumfari babban Birnin Kasar
- Yanzu haka manyan motocin yaki sun shiga Harare
- Ana dar-dar tsakanin Soji da ‘Yan Jam’iyyar ZANU
Mun samu labari daga Jaridun Kasar waje cewa yanzu haka Sojoji a Kasar Zimbabwe sun dumfari babban Birnin Kasar na Harare.
Shugaban Kasar Zimbabwe Robert Mugabe
Dama kun ji cewa cewa Sojoji sun ja kunnen Shugaban Kasar Zimbabwe watau Robert Mugabe da ya dade yana mulki a jiya. Yanzu haka manyan motocin yaki sun shiga Harare inda su ke ta rufe manyan hanyoyi na Birnin kamar yadda Jaridar Independent ta rahoto.
Shugaban Kasa Robert Mugabe ya zargi Shugaban hafsun Soji na Kasar Janar Constantino Chiwenga da kokarin cin amanar Kasa. Kwanan nan Mugabe ya sauke Mataimakin sa Mr Mnangagwa wanda ta sa Sojojin su ka ja kunnen Jam’iyyar da ke mulki a Kasar.
An kusa yin zabe a Kasar Zimbabwe da tun da aka kafa ta Robert Mugabe yake mulki. Wasu na ganin Shugaban mai shekaru 93 a Duniya yana kokarin ganin Mai dakin sa ta dare mulkin kasar ne yayin da shi kuma yake shirin barin mulkin wanda ya kawo dar-dar a Kasar.

Labels: