Sanatan dake wakiltar mazabar majalisar dattijai ta Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani kuma fitaccen dan gwagwarmaya ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari fa ya riga da ya zagaye kan sa da mahandama da babakere sannan kuma yana bukatar agajin gaggawa.
Sanatan yayi wannan ikirarin ne a yayin wata fira da yayi a gidan rediyon RAVE FM a garin Osogbo lokacin da yake gabatar da wata kasida tare da sharhi game da yadda gwamnatin nan ke yakar cin hanci da rashawa.
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
Hausansi dai ta samu cewa Sanata Shehu ya jaddada cewa baya shakku to tababar yakinin shugaba Buhari wajen yin yaki da rashawa tun daga zuciyar sa amma tabbas ya san na zagaye dashi hakan bai kai zuciyar su ba.
Daga nan ne ma dai sai ya shawarci 'yan kasa dukkan su da su dukufa wajen yiwa shugaban addu'ar Allah ya kubutar dashi daga hannun su.
Labels: Labarai