'Yan Shi'a sun ce a tono musu gawawwakin 'yan uwansu da aka turbude a ramuka

Sojoji sun kama Zakzaky yau shekara biyu kenan ba labari

- Shi'a sun shigar da kara zuwa kotun duniya, kuma sun nemi goyon bayan AU, EU, UN, ECOWAS

- Sun nemi a tono musu gawawwakin 'yan uwan su don su yi musu jana'iza

'Yan Shi'a, a karkashin jagorancin kungiyar tattakin Islama ta Najeriya (IMN), sun bukaci a tono musu gawawwakin 'yan uwan su da sojoji suka musu kisan gilla a Zaria, sannan suka haka manyan ramuka suka turbude su.

Mai magana da yawun bakin kwamitin neman 'yancin Zakzaky, Abdulhamid Bello, ne ya yi wannan kira a taron 'yan jaridar da aka yi a Kaduna, wanda ya dau taken "Shekara biyu bayan kisan gilla a Zaria da kuma tsare Sheikh Zakzaky."

'Yan Shi'a na zanga-zangar a sako musu Zakzaky

Bello ya ce suna so ne a tono su don su tantance wadanda aka kashe don a sanar da iyalan su, sannan kuma a yi musu jana'iza ta musulunci.

"A cikin shekaru biyun da suka wuce, an hana mu sakat mu gudanar da addinin mu yadda ya kamata. Saboda wannna, a yanzu haka mun shigar da kara a kotun duniya ta The Hague, a Nezaland, kuma har sun bude bincike a akai.

"Muna kira ga majalisun dinkin duniya da nahiya, UN, EU, AU da ECOWAS, da su hada kai da kotun duniya don su tilastawa gwamnatin Najeriya da su saki Zakzaky sannan kuma su bar mu muyi addinin mu."

Ya gama da cewa. "Duk wanda yake da hannu tsangwamar da ake mana da kisan gillar da ake mana zai shiga hannun hukuma nan kusa, duk mulkin sa."

A harin da sojoji suka kai musu a Zariya, an kama shugaban Shi'a Sheikh Ibrahim Zakzaky, da matar sa, da kuma wasu mukarraban sa, wadanda har yanzu suna nan a kulle.

Labels: