Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya nuna kulawa kan al’amarin rikicin maáurata a arewacin Najeriya, musamman akan mata.
Sarkin yayi tsokacin ne a ranar Jumaá a wajen bude taron kungiyar mata musulmai na kasa (FOMWAN) karo na 32 a Kano.
Ya ce abun damuwa ne yadda wasu mutane suka juya littafi mai tsarki don kawai su cimma wasu munanan manufarsu akan mata.
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
A cewar sa, kimanin mako daya day a gabata, a nan Kano, wani mutumi ya yi wa matarsa duka har lahira sannan cewa wannan misali daya ne cikin misalai da dama na abubuwan dake faruwa da mata a gidan aure.
Ya yi kira ga hukumomi da su hada kai da fata, wajen magance matsaloli da mata da yara ke fuskanta.
Labels: Labarai