Shahararren jarumin Kannywood, Ali Nuhu ya nada wata matashiyar tauraruwar Fim, Teemah Makamashi sarautar Jakadiyar FKD, kamfanin Fina Finan Ali Nuhu.
Wannan bikin nadin sarautar ta gudana ne a ranar Talata 28 ga watan Nuwamba, wanda ya samu halartar yan uwa da abokan arziki daga sashin Kannywood.
Teemah, jakadiyar FKD
Shafin ‘Kannywood Scene’ ta bayyana daga cikin wadanda suka halarci kasaitaccen bikin akwai Haliman Saima, Rukayya Dawayya, Jamila Nagudu, Adam A Zangoa, Abba Al-Mustapha da sauran jaruman Kannywood.
Teemah
Majiyar hausansi ta ruwaito a yayin bikin, Jarumi Ali Nuhu ya bayyana kokari da hazakar Teemah a matsayin wasu daga cikin abubuwan da suka ja hankalinsa wajen nada wannan muhimmin sarauta.
Bikin
Bikin