Boss Mutsapha ya ziyrci tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya a jamhuriyya 2 Alex Ekueweme a asibitin Landan inda yake jinya
- Helen Alex Ekwueme,ta anshi bakoncin Boss Mustapha a madadin iyalan tsohon mataimakin shugaban kasar
- A makon da yagabata ne shugaba Buhari ya ba da umarnin fitar Alex Ekueweme kasar waje jinya bayan ya yanke jiki ya fadi a gidan sa
Seketaren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya ziyarci tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya a jamhuriyya na biyu Dakta Alex Ekueweme a asibitin Landan inda yake jinya.
Mustapha ya mika sakon gaisuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari ga Dakta Alex Ekwueme.
Matar dakta Alex Ekueweme Helen Alex Ekwueme ta anshi bakoncin Boss Mustapha a madadin iyalan tsohon mataimakin shugaban kasar.
Seketaren gwamnatin tarayya ya ziyarci Alex Ekwueme a asibitin Landan
Hadimin shugaban kasa na fannin watsa labaru a Malam Garba Shehu, ya sanar da haka a shafin sa na Tuwita a ranar Litinin 13 ga watan Nawumba.
A makon da ya gabata ne shugaba Buhari ya ba da umarnin fitar da tsohon shugaban kasa dakta Alex Ekwueme zuwa Asibitin birnin Landan jinya dan samun kyakyawar kulawa.
Umarnin ya zo ne mako daya bayan Alex Ekwueme ya yanke jikin ya fadi a cikin gidan sa dake jihar Enugu a ranar 26 ga watan Okotoba
Labels: Labarai