Sabon Salo: Wani Ango da Amarya sun isa wurin liyafar bikin su a mota Tifa

Jama'a da dama dai kan kashe kudin yayin bikin su domin birge 'yan uwa da abokan arziki dama mutanen gari. Ango da Amarya kan shiga mota mafi kyau da tsada lokacin bikin su. Amma abin ba haka yake ba a wurin wani Ango da Amaryar sa 'yan asalin Jihar Akwa Ibom da suka zabi yin zir-zirgar biki cikin motar dakon yashi wato Tifa.

Wani Ango da Amarya sun isa wurin liyafar bikin su a mota Tifa

An dai shirya Tifar da kwalliya mai kayatarwa kamar yadda ake yiwa motar duk wani Ango da Amarya yayin bikin su.

Wani Ango da Amarya sun isa wurin liyafar bikin su a mota Tifa

Ba a ambaci sunan Angon ko Amaryar ta sa ba, amma dai ga hotunan su nan kamar yadda kuke gani.

Wani Ango da Amarya sun isa wurin liyafar bikin su a mota Tifa

Wani Ango da Amarya sun isa wurin liyafar bikin su a mota Tifa

Labels: