Sama da mutum 400 na Likitocin waje sun fadi jarrabawa fara aiki a Najeriya
- Likitoci 680 da su kayi karatu a waje su ka zana jarrabawar kwanan nan a Kasar
- Da dama dai sun sha kasa amma sun ce da gan-gan a kada su ba wani abu ba
Labari ya kai gare mu cewa sama da Likitoci da dama da su kayi karatu daga Jami’o’in Kasar waje sun fadi jarrabawar samun damar yin aiki a asibiti a Najeriya da aka gudanar kwanan nan.
Likitocin waje sun gaza cin jarrabawa aiki a Najeriya
BBC Hausa ta rahoto cewa Likitoci sama da 400 da su kayi karatu a kasar waje sun fadi jarrabawa a Najeriya. Likitoci 680 ne dai su ka rubuta jarrabawar daga cikin wadanda su kayi karatun koyon aikin Likitancin na su a kasashen waje.
Wasu daga cikin su dai sun yi karatu ne a irin su a Kasar Misra. ‘Yan Najeriya na fita kasashen Sudan da kuma Uganda domin zama Likitoci amma ga shi kuma da dama daga cikin su, sun gaza jin jarrabawar da ake yi a Najeriya kafin a fara aiki.
Sai dai kamar yadda labarin ya zo mana Daliban sun koka da lamarin inda su kace an kada su jarrabawar ne ba bisa ka’ida ba inda ma iyayen wasu yaran su ka shirya zuwa gaban Majalisar Dattawan Kasar domin kai kukan su kwanan nan.
Labels: Labarai