Shugaban hafsan soji, Janar Tukur Buratai ya kawata sababbin manjo janar 44 da aka karawa girma
- An gudanar da bikin Karin girman ne a dakin taron masaukin sojoji dake Maiduguri, jihar Borno
- Masoyan jami’an da akayi wa Karin girma sun halarci taron don taya su murnar sabon matsayinsu
A ranar Talata 28 ga watan Nuwamba, Shugaban hafsan soji, Janar Tukur Buratai ya kawata sababbin manjo janar 44 da aka karawa girma.
Hausansi ta tattaro cewa an gudanar da bikin Karin girman ne a dakin taron masaukin sojoji dake Maiduguri, jihar Borno.
Da yake jawabi Janar Tukur Buratai ya bayyana cewa an zabi gudanar da taron domin karfafawa jami’an Operation Lafiya Dole gwiwa.
An yi wa wasu Sojojin Najeriya karin girma
Haka zalika an an yabawa wadanda suka samu wadannan matsayi tare da sauran jami'an sojin da basu samu mukamin ba, inda aka karfafa musu gwiwa bisa namijin kokarin da jarimta da suke yi wajan tabbatar da tsaro a fadin kasar musamman a yankin Arewa maso gabas.
Karin hotuna daga taron:
An yi wa wasu Sojojin Najeriya karin girma
An yi wa wasu Sojojin Najeriya karin girma
Labels: Labarai