7Gwamnan jihar Anambra Cif willie Obiano, ya bayyana damuwar sa kan yadda aka zare jami'ai da suke bashi kariya, inda ya ce wannan lamari ya jefa rayuwar sa cikin hatsari.
Obiano wanda ya bayyana hakan a ranar Talatar da ta gabata yayin ganawa da masu ruwa tsaki a taro wanda hukumar zabe ta kasa ta dauki nauyin shirya wa, ya bayyana rashin amince wa da wannan abu da kuma cewar barazana ce ga rayuwar sa sakamakon gabatowar zaben gwamna na jihar.
Gwamnan ya bukaci da a maido da jam'ai masu bashi kariya domin gujewa barazanar hatsari ba gare shi kadai ba domin kuwa har al'umma. Ya kuma ce duk wanda ke da hannu a cikin wannan lamari sai sun kunya domin kuwa sun shirya wa wannan zabe.
A cewar gwamnan, ya kamata su tattauna da sufeto janar na 'yan sanda akan lamarin, sai dai an yi rashin sa'a bai halarci taron ba, wanda hakan ya sanya shi bayyana hakan a bainar jama'a.
Gwamnan ya kuma nuna irin rashin jin dadi yadda ba a ko kula da zuwan shi taron ba, inda shugaban hukumar zabe Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa, wannan taro ne na masu ruwa da tsaki saboda haka babu wani dan takara da za a baiwa fifiko duk da irin mukamin sa.