Musayar yawu tsakanin fadar Shugaban kasa da Sule Lamido ya dauki sabon salo


An cigaba da cacar baki tsakanin fadar shugaban kasa da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, inda ranar Talata 14 ga watan Nuwamba, Lamido ya soki Kaakakin shugaban kasa Garba Shehu.
Daily Trust ta ruwaito Lamido ya bayyana Garba Shehu a matsayin wanda ke kokarin samun gindin zama tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Lamido ya mayar da martani ne biyo bayan jawabin da Garba Shehu yayi, wanda shima martani ne ga Lamido, inda yace bai kamata yan Najeriya su saurari Sule Lamido ba, saboda yana da guntun kashi a gindinsa na satar kudaden jihar Jigawa.
Ta bakin hadiminsa na bangaren kafafen sadarwa na zamani, Mansur Ahmed, yace sun fahimci Garba Shehu ya gagara amsa zarge zargen da Sule Lamido yayi ma gwamnatin Buhari, don haka ne ya koma yana cin mutuncn masu mutunci.
“Idan Garba na magana akan sanin ya kamata ne, me ya hana shi fita daga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, a gani na kawai yana gogoriyon samun fada ne a wajen Buhari.” Inji Lamido.
Lamido yace ba zai daina fadin albarkacin bakinsa ba a duk abubuwan da suka shafi Najeriya, saboda shi dan Najeriya ne, kuma yana da damar yin hakan a tsarin mulkin kasar.

Labels: