Matsalar da ke tattare da tsoho ya auri karamar yarinya

Shugabar mata a hukumar Hisbah ta jihar Kano, Dr Zahra’u Muhammad Umar, ta sanar da illolin dake tattare da aura ma yara mata mazan aure tsofaffi.

A cewarta ta sha fadakarwa akan al’amarin aura ma kananan yara maza tsofaffi, inda ta sanar da cewa harma ta sha yin muhawara da malaman addini dake kare irin wannan muradi.

Illar da ke tattare da tsoho ya auri karamar yarinya

Kusan za a iya cewa auren karamar yarinya ga tsoho wani al’amari ne da ba kasafai ake zantawa akan shi ba saboda rashin haramcin yin haka a addini da ma al'ada.

To sai dai Dr Zahra'u ta ce duk da cewa addini bai haramta irin wannan aure ba amma zamani da irin illolin da ke tattare da wannan aure ka iya sa a sanya masa ayar tambaya.

A cewar ta da zaran namiji ya kai shekaru sittin zuwa saba'in karfin sa na da namiji zai fara raguwa yayinda ita kuma mace a lokacin ne take dauke da ganiyar kuruci. Don haka ana iya samun matsala ta nan.

Labels: