- Hukumar EFCC ta sanar da cewa Matashin da ya fallasa kudaden gidan Ikoyi ya zama Miloniya
- Magu ne ya tabbatar da hakan a Austria
- Ya ce a yanzu haka ana horar da matashin kan yadda zai sarrafa kudin
Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta sanar da cewa matashin da ya yi tsegumi kan inda aka boye makudan kudin nan da yawansu ya kai dala miliyan 43.4 a wani gida dake yankin Ikoyi na jihar Lagas ya zama miloniya a yanzu haka.
Shugaban hukumar ta EFCC, Ibrahim Magu ne ya tabbatar da wannan ci gaba da matashin ya samu a Vienna, Austria, a ranar Alhamis.
A kokari da ake na kawo karshen cin hanci da rashawa, gwamnati ta billo da sabon hanya, ta yadda duk mutumin da ya taimaka aka gano inda kudaden sata suke, zai samu kaso 2.5 na kudaden da aka gano.
A cewar Shugaban EFCC, a halin yanzu ana ci gaba da ba matashin horo na musamman kan yadda zai sarrafa kudaden saboda bai taba ganin irin wadannan kudade a rayuwarsa ba.
Labels: Labarai