Masu yiwa Kasa hidima 21 sun fuskanci hukunci a jihar Kano

Hausansi ta samu rohoto da sanadin jaridar The Nation cewa, akwai masu yiwa kasa hidima 21 a jihar Kano da za su maimaita hidimar su sakamakon rashin da'a da kiyaye dokokin da suka nuna yayin gudanar da hidimar ta su cikin shekara guda.
Shugaban hukumar ta yiwa kasa hidima reshen jihar Kano Alhaji Ladan Baba ne ya bayyana wa 'yan jarida na kaffanin dillancin labarai na NAN, a yayin da ake gudanar da bikin yaye masu yiwa kasar hidima a ranar Alhamis din da ta gabata.
Ya ke cewa, an samu masu yiw kasa hidima 21 da suka nuna rashin da'a wajen gudanar da hidimar ta su, sakamakon haka za su maimata makonni ko watanni dangane da irin laifinsu.
Masu yiwa Kasa hidima 21 sun fuskanci hukunci a jihar Kano
Shugaban ya kuma nuna damuwar sa akan yadda suka yi rashi na masu yiwa kasa hidima biyu, inda ya bayar da sunayen su kamar haka; Shu'aibu Yahuza daga jihar Bauchi sai kuma Happiness Emmanuel daga jihar Enugu.
Ya bayar da sanarwar cewa akwai masu yiwa kasa hidima 2, 574 da su kammala hidimar ta su, kuma akwai 13 daga cikin su da suka nuna kwazo da bajinta yayin gudanar da hidimar ta su, wanda gwamnatin jihar Kano za ta basu kyaututtuka.
A karshe ya kuma jinjina wa gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje dangane da iri fadi tashin da gwamnatin sa take yiwa masu hidimar ta kasa.

Labels: