
Masana da dama na ganin cewa kasafin kudin da ya gabatar na shekarar 2018 a kwanan bayana a gaban majalisar tarayyar Najeriya ba zai iya wani yin katabus ba ga cigaban rayuwar talaka kamar dai yadda Mista Bismarck Rewane ya kwarmata a yayin taron masana a satin da ya gabata.
Masanan da dama dai na ganin cewa maimakon shugaban kasar ya karkatar da kasafin kudin ga lamurran da za su kawo cigaba kai tsaye musamman ma a harkar tattalin arziki, amma sai suka ga akasin hakan.
Masana sunyi fata-fata da kasafin kudin shekarar 2018 na Buhari
Hausansi dai ta samu cewa masanan da suka halarci taron da aka gudanar sun hada da wani Farfesa a jami'ar tarayya ta Legas, mai suna Ifeanyi Nwokoma sai kuma babban Darakatan hukumar tattalin arziki da kasuwancin jihar ta Legas Mista Muda Yusuf sai kuma Mista Mounir Gwarzo.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa shugaban kasar ta Najeriya ya gabatar da kasafin kudin shekarar ta 2018 na sama da Naira Tiriliyan 8 a gaban majalisar tarayya a ranar Litinin din da ta gabata.