Majalisar dattijai ta bankado badakalar Dala miliyan 350 a karkashin minista Fashola

Rigimammen dan majalisar dattijan nan mai wakiltar mazabar jihar Kogi ta yamma mai suna Sanata Dino Melaye ya zargi ma'aikatar samar da wutar lantarki karkashin kulawar ministan Buhari Babatunde Fashola da kashe makudan kudaden da suka kai Dala miliyan 385 ba bisa ka'ida ba.
Sanatan dai yayi wannan ikirarin ne a zauren majalisar yau Alhamis 2 ga watan Nuwamba yayin da yake yin tsokaci game da lamarin da aka yi wa lakani da 'shirin samar da wutar lantarki da sauri' da aka tsara gina wasu sabbin tashoshin samar da wutar a fadin kasar.
Hausansi ta samu dai cewa Sanatan yayi ikirarin cewa ma'aikatar wutar lantarkin ta kashe makudan kudaden ne ba tare da amincewa zauren majalisar ba da kuma ya bayyana cewa babban sabo ne a kundin tsarin mulkin kasa.
Haka ma dai Sanatan ya kuma koka kan yadda yace a ka shafe shekaru da dama akasar nan ana fitar da makudan kudade da nufin kasa samar da hasken wutar lantarkin amma har yanzu ba amo ba labari.

Labels: