Maikanti Baru ya ciri tuta a nahiyyar Afirka, Karanta abin alfahari da yay

Manajan Darakta na kamfanin man fetur (NNPC) dakta Maikanti Baru, ya lashe kyautar babban Kamfanin sadarwa dake birnin New York na gwarzon man fetur da gas a shekarar 2017 na nahiyyar Afirka baki daya.

An samu wannan rahoton ne da sanadin Mujjalar Forbes wanda shugaban ta Mark Furkon ya bayyana tun a ranar 11 ga watan Oktoba.

Mujallar Forbes ta bayyana cewa, wannan kyauta ana lashe ta ne yayin da kiddiga ta bayyana mutumin da kere kowa jajirce wa akan harkokin man fetur da gas wajen bayar da gudunmawa ta ci gaban sashen tare da daidaiton tattaliin arzikin da suke gudanarwar su akai.

Maikanti Baru

Hausansi ta fahimci cewa, Baru ya lashe wannan kyauta ne sakamakon irin fadi tashin da yake yi a matsayin sa na shugaban kamfanin NNPC cikin shekarun da suka shude.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan bikin bayar da kyautar ya samu halarta ta manyan kamfanonin man fetur, masu kawo tsare-tsare, 'yan kasuwanni da kuma 'yan siyasa da dama

Cikin watanni 18 da ya shafe akan kujerar shugabancin kamfanin na Man fetur, Dakta Baru ya samu kyatuttuka daban-daban sakamakon irin nagarta ta jagorancin sa.

Labels: