
- Hukumar tsaftace muhalli ta jihar Borno ta dauki nankasassu aikin sharan tituna a jihar
- Hukumar ta ce mafi yawan wadanda aka dauka yin aikin a Maiduguri guragu ne akan albashin naira 10,000
- Daya daga cikin guragun ya ce barar ta ishe su, cewa masu kafa ne yanzu suke bara
Hukumar tsaftace muhalli ta jihar Borno ta dauki nankasassu aikin sharan tituna a jihar. Mafi yawan wadanda aka dauka yin aikin a Maiduguri guragu ne akan albashin naira 10,000 a kowane wata, kuma bisa ga alamu guragun sun gwammace aikin da yawon barace-barace.
Kamar yadda Hausansi ke da labari, nakasassun na sanye da wasu kaya na musamman da hukumar tsaftace muhalli a jihar ta basu wanda za su rika amfani da ita a duk lokacin yin aikin.
Daya daga cikin ma’aikatan, Muhammad Abubakar ya shida wa muryar Amurka cewa duk wani mai lallura ana ganin tamkar mabaraci ne, amma su barar ta ishesu, kuma ya ce masu kafa ne yanzu suke bara. Dalilin da yasa suka nemi aikin da masu kafa ke kyamar yi.
Guragu masu sharan tituna a Maiduguri
Alhaji Abdulrahaman Kwankwasiya wanda shi ma nakasasshe ne a cikin masu sharan ya ce ya yi matukar murna da samun aikin.
Shugaban guragu a jihar Borno, Mallam Alfaki Idris a nasa bangare ya ce kamar yadda ake biyan duk wani ma’aikacin tsaftace muhalli a jihar kudi naira 10,000 a kowane wata, haka su ma ake biyansu.
Shugaban ya roki gwamnan jihar Kashim Shettima da ya mayar dasu ma’aikatan din-din-din.
Shugaban hukumar tsaftace muhalli ta jihar, Alhaji Nasiru Ali ya bayyana dalilin da ya sa suka dauki guragun aiki. Ya ce rikicin Boko Haram ya sa mutane da yawa sun rasa abun yi duk da bukatar dake akwai na karewa kowa hakkinsa, shi ya sa aka dauki nakasassun aiki.