Hukumar EFCC ta shiga Kotu da wasu Ma’aikatan INEC na kasa
- Ana zargin su da karbar kudi daga hannun Mrs Diezani Madukwe
- Tsohuwar Ministar ta karkatar da kudi domin lashe zabe a 2015
Kamar yadda labari ya zo mana wasu Ma’aikatan Hukumar zabe na INEC sun shiga hannu bisa zargin karbar kudi daga hannun Diezani Alison-Madukwe.
Wasu Jami’an INEC da su ka karbi kudi a 2015
Diezani Alison-Madukwe ta rike Ministar man fetur a lokacin tsohon Shugaba Jonathan Goodluck inda ake zargin ta da satar makudan dukiyar kasar. Ana zargin Diezani da karkatar da wasu Dala Miliyan 115 na kudin kasar wajen harkar neman cin zabe.
Yanzu haka Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin kasa zagon-kasa ta damke wasu Manyan Ma’aikatan Hukumar zabe na Kasa INEC Auwal Jibrin da wani Ma’aikacin wata kwalejin Kasar Garba Ismail inda tayi Kotu da su bisa zargin cin wadannan kudi a 2015.
Mun samu labari daga Jaridun kasar nan cewa kwanaki tsohuwar Ministar man Mrs. Diezani Madukwe ta nemi Kotu ta bata dama ta dawo Najeriya domin ta wanke kan ta daga zargin da ke wuyan ta.