Mai'aikatar tsaron Najeriya a yau din nan ta fitar da sanarwa tana mai karyata wani rahoton da wata jarida ta fitar inda ta zarge ta da wata badakalar makudan miliyoyin daloli da tace mahukuntan hukumar sunyi dumu-dumu a ciki wadda take da alaka da gina wata asibiti a kasar Mali.
Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Kanal Tukur Gusau ya sanyawa hannu ya kuma rabawa manema labarai a Abuja, babban birnin tarayya.
Ma'aikatar tsaron Najeriya ta musanta zargin badakalar kudin da ta kunno kai
Hausansi ta samu dai cewa ma'aikatar ta cewa wannan labarin bai da tushe balle makama sannan kuma ta roki jama'a da suyi fatali da shi.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa mun kawo maku rahoton cewa wata 'yar karamar husuma ta tashi tare da rarrabuwar kawuna a tsakanin manyan ma'aikatan gwamnati yayin da aka bankado wata sabuwar badakalar makudan kudaden da suka tasar wa dalar Amurka miliyan 1.4 a ma'aikatar tsaron Najeria domin yin ayyukan majalisar dinkin duniya.