Daga
karshe ma’aikatar tsaro ta saki kudade don biyan alawus na rundunar sojin Najeriya dake yaki da yan ta’addan Boko Haram a Arewa maso gabas da kuma wadanda ke gudanar da ayyuka daban daban a fadin kasar.
A wata sanarwa da ya saki a ranar Litinin, kakakin rundunar soji, Birgediya Janar Sani Usman yace shugaban hafsan soji Tukur Buratai yayi umurni gas akin kudin a ranar Litinin.
A ranar Lahadi ne, Buratai ya aika wani sako na musamman don bayar da tabbaci da kuma karfafa ma sojoji gwiwa a aiki da suke a gida da wajen kasar.
Hakan ya biyo bayan korafi da sojoji dake yakar ta’addanci a arewa maso gabas suka yi kan cewa basu samu alawus dinsu na tsawon watanni biyu ba.