Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ba mabiyansa damar barin jam’iyyar All Progressives Congress (APC)
- Dan dan’uwansa Musa Iliyasu Kwankwaso ne ya sanar da hakan
- An rahoto cewa an ba mabiyan nasa damar sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP)
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso y aba mabiyansa damar barin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Dan dan’uwansa, Musa Iliyasu Kwankwaso, ne ya bayyana hakan, duk da cewan akwai rade-radin cewa Kwankwaso na iya barin jam’iyyar APC.
Iliyasu Kwankwaso, wanda ya kasance kwamishinan ma’aikatar ayyuka na musamman a jihar Kano, ya fada ma jaridar Daily Trust cewa Kwankwaso a shirye yake ya koma jam’iyyar PDP domin cimma kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa tunda ya kasa cimma hakan a APC.
Rahotannin kafofin watsa labarai sun nuna cewa manyan yan PDP sun sa wa tsohon gwamnan matsin lamba kan ya dawo jam’iyyar.
A cewar Iliyasu Kwankwaso, sanatan dake wakiltan Kano ta tsakiya, ya rigada ya bukaci mabiyansa da su koma jam’iyyar PDP.