Musa Ilyasu Kwankwaso ya yabawa Mai Girma Gwamna Ganduje
- Kwankwaso yace sai tsohon Gwamnan Kano yayi da gaske a 2019
- Musa Kwankwaso ya bar PDP ya koma tare da Gwamna Ganduje
Za ku ji cewa wani Kwamishinan Jihar Kano Musa Ilyasu Kwankwaso yace tsohon Gwamna Rabi’u Kwankwaso ya rikice da neman takarar Shugaban Kasa kuma ba zai kai labari ba a zaben 2019. Ilyasu Kwankwaso 'Danuwan tsohon Gwamnan ne.
Musa Ilyasu Kwankwaso ya yabawa Gwamna Ganduje
Musa Ilyasu Kwankwaso wanda Kwamishina ne yanzu haka a Gwamnatin Jihar Kano ya yabawa Gwamnan Jihar na Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje wanda yace mutum ne mai matukar saukin kai kuma bai yarda da tada rikici ko rike mutum a zuciya ba.
Kwankwaso a hirar da yayi da Jaridar Daily Trust yake cewa a zaben 2015, mutanen Kano sun zabi Abdullahi Ganduje ne da Shugaba Buhari wanda yace haka za a kara yi a zaben 2019 don haka tsohon Gwamna Kwankwaso ya daina bata lokacin sa a banza.
Musa Kwankwaso yake cewa idan ba ayi wasa ba Sanata Kwankwaso zai yi biyu-babu don haka gara ya hakura da neman Shugaban kasa yayi kokarin rike kujerar Sanatan sa. Kwankwaso yace irin kokarin Ganduje ta sa ya shigo Jam’iyyar APC daga PDP mai adawa.
Ko da cewa 'Yan kauye daya ne, sai dai Musa Kwankwaso da Rabi'u Kwankwaso sun sha bam-bam a siyasa. Kwamishinan yace Kano ta Ganduje ce da Buhari a 2019.
Labels: Labarai