Wata kotun majistare dake zaman ta a unguwar Tinubu a jihar Legas a jiya Laraba ta mayarwa da da dan tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar mai suna Abubakar Atiku hurumin ci gaba da rikon 'ya'yan sa biyu da a da tsohuwar matar sa Fatima Bolori ta karba.
Alkalin kotun dai mai suna Kikelomo Ayeye shine ya yanke hukuncin inda ya bayar da umurnin mahaifin su ya cigaba da daukar nauyin yaran da yanzu haka suke karatu a wata makaranta a garin Legas din.
Hausansi ta samu dai cewa duk da yake ba'a bar yan jarida sun shiga zaman kotun ba, amma wani wanda aka yi zaman kotun da shi ya bayyanawa majiyar mu cewa Alkalin ne da kansa ya hannanta ma Abubakar Atiku din yaran.
Mai karantu dai zai iya tuna cewa a satin da ya gabata ne dai wata kutun ta bayar da umurnin cewa ya'yan su koma hannun mahaifiyar su bayan mutuwar auren nasu.