Sun yi fashin babur
- Mukarraban sa sun tsere sun bar shi
- Za'a ci gaba da shari'a a Disamba
A ranar Alhamis kotun Sango-Ota, a jihar Ogun, ta garkame wani saurayi, Isamaila Jimoh, dan shekara 22 a gidan wakafi bisa zargin fashi da makami.
Alkalar da ta saurari karar, Mis B. B. Adebowele, ta ce a ajiye mata shi zuwa a gama bincike, a dawo sauraron karar a ranar 21 ga Disamba.
Kotu ta garkame shi saboda fashi da makami
Ana zargin Jimoh da hadin-baki da wadansu mukarraban sa don a yi wa wani Musa Ali fashin babur din sa kirar Bajaj, wanda ya kai kimanin N205, 000. Wannan ya auku ne a ranar 8 ga Satumba a tashar 'Arise and Shine' a Itele, Ota, da misalin karfe 10.30 n.d.
Ragowar abokan na shi sun bar shi hannun hukuma
Jimoh ya keta sashi na (1) (2) (a) na hukunce-hukuncen dokokin kasa.