-Shugaban Kasa Buhari ya bayyana irin ayyukan da yayi wa Inyamurai
- Garba Shehu ya jero ayyukan more rayuwa da Gwamnatin nan ke yi
- Yau ne Shugaban Kasar zai leka Yankin kudu maso gabashin Kasar
Mun samu labari cewa a jiya ne Fadar Shugaban kasa ta bayyana irin goma sha tara na arzikin da Shugaba Muhammadu Buhari yayi wa Yankin Inyamurai a mulkin sa.
Shugaban kasa Buhari na Inyamurai ne Inji Garba Shehu
Mai magana da yawun Shugaban Kasar watau Malam Garba Shehu ya jero da dama na ayyukan more rayuwa da Gwamnatin Shugaba Buhari ke yi a Yankin Kudu maso gabashin Kasar salin-alin. Shehu ya bayyana wannan ne a wani rubutu da yayi.
Shugaba Buhari zai leka Jihar Ebonyi domin kaddamar da wasu ayyukan Gwamnati sannan kuma ya wuce Jihar Anambra inda zai daga hannun ‘dan takarar Jam’iyyar APC Tony Nwoye. Wasu dai na yada cewa Shugaban ba yayi da mutanen Inyamuran.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari dai yana ta ayyukan tituna a Yankin Kudancin kasar na sama da kilomita 600. Sannan kuma Gwamnatin sa ta dukufa a harkar noma a Kasar ban da maganar ayyukan ruwa da kuma manyan Ministoci da ya ba Yankin.
Labels: Labarai