Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya zai fada hannun EFCC
- Kwanan nan Shugaban Kasa Buhari ya sallami Babachir Lawal
- Shi ma Shugaban Hukumar tsaro na NIA Ayo Oke bai sha ba
Mun samu labari cewa Hukumar EFCC za ta binciki tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir Lawal da aka sallama a farkon makon nan bisa zargin lashe wasu Naira Miliyan 200 na kwangila.
Kamar yadda labarin ya zo mana daga Gidan Talabijin nan na Channels TV, Hukumar EFCC mai yaki da masu yi tattalin arzikin kasa zagon kasa ta fara shirin binciken zargin da ke kan tsohon Sakataren Gwamnatin Buhari watau Mr. Babachir David Lawal.
Ana zargin Babachir da buga badakala a wasu kwangiloli da Gwamnati ta bada a Yankin Arewa maso gabashin Kasar inda Majalisar Dattawa ta bada shawarar a tsige sa bayan gudanar da bincike. Yanzu haka EFCC ta shirya kwamiti domin binciken wadannan zargi.
Kwanan nan EFCC ta gayyaci tsohon Shugaban na Hukumar Ambasada Ayo Oke shi ma bisa zargin da ke kan sa. Dama dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fadawa Hukumomin su yi ram da Babachir Lawal da Ayo Oke kamar yadda doka ta tanada.