Gwamnantin kasar Amurka ta yi ikirarin cewa akwai daruruwan miliyoyi na dala da gwamnatin Najeriya ta boye a lokacin mulkin marigayi shugaban kasa na mulkin soja, Sani Abacha.
A ranar Talatar da ta gabata ne, Lauyan kolu kuma ministan Shari'a Abubakar Malami, da shahararren lauya mai kare hakkin dan Adam, Femi Falana, suka bayyana hakan a jihar Legas.
Malami da Falana wanda duk mahalarta wani taro ne da shirin yaki da cin hanci da rashawa na SERAP ya gudanar akan samar da hanyar dawowa da Najeriya kudaden ta da aka sace kuma aka yi ajiyar su a kasashen ketare.
Marigayi Sani Abacha tare da shugaban kasar Amurka Donald Trump
Lauyan kolu wanda babban hadimin sa akan aikata kananan laifuka Mista Abiodun Aikomo, ya tir da kusoshin gwamnati dake sace kudin kasa kuma su na ajiyar su a kasashen ketare.
Ya ke cewa, gwamnatin Najeriya tun shekaru da dama da suka gabata take tuntubar shawarwari akan dawo ma ta da kudaden da aka sace na kasa.
Kasar ta Amurka ta bayyana a kotun wata kasa da cewar tana da sha'awar wannan kudade domin kuwa an yi ajiyar su ne a dalolin kasar su.
Shi kuwa Falana ya zargi kasashen Amurka, Switzerland, Birtaniya da wasu kasashen na Yamma, akan dabi'u na banza da suka dauka wajen dawo wa da Najeriya kudaden ta dake makire a bankunan su, ya kuma ware kasar Amurka a matsayin jagoran dangane da wannan dabi'a ta Allah wadai.
Ya ke cewa, "Najeriya ta bankado wani bangare na kudaden da Abacha ya wawushe kuma ya yi boyon su a birnin Jersey na kasar Amurka, sai dai kasar ta Amurka ta yi ikirari a kotu da cewar ba za ta sakarwa Najeriya kudaden ba."
"Yayin da kotu ta tuntuba, kasar Amurka ta ce sai dai ta baiwa gwamnatin Amurka wannan kudade domin ta yiwa Najeriya amfani da su ta hanyar da ta ke ganin ya cancanta."