Kannywood: Ana tsula tsiya na kin-karawa a cikin harkar fim – Zango

- Adam Zango yace akwai mutanen banza a ‘yan fim

- Dan wasan yace ana buga fasikanci na kin karawa

- Tauraron yace akwai fa gyara a harkar kannywood

Mun samu labari cewa babban Dan wasan nan Adam A Zango ya kalubalanci ‘Yan fim din Hausa inda yace akwai gyara.

Tauraron Dan wasa Adam Zango

Gwarzon ya tabbatar da cewa dai akwai bata-gari a cikin ‘Yan fim da dama kamar yadda ake samun na banza a ko ina a Duniya. Dan wasan ya tabbatar da cewa wasu ne su ka jawo wasu har ta kai ake kiran su jahilai da sauran su a fagen fim.

Adam Zango ya kuma bayyana cewa masifar da ke cikin Kannywood ta wuce duk yadda ake tunani inda yace ana buga zalunci da fasikanci iri-iri. Yace sai ka ga yara daga fara fim sun kuma bude na su kamfanin har sun zama manya.

Zango ya bayyana wannan ne a shafin sa na Facebook inda yace idan fa abin da ya fada karya ne sai a tona masa asiri amma shi ba zai kama sunan kowa ba.

Labels: