Wannan al'amari ya faru ne a gaban wata kotu da ke zama a garin Abeokuta
- Mutumin ya bayyana gaban kotun ne ya na neman rabuwa da matar sa
- Ya ce tsoro ne ya mantar da shi sunayen 'ya'yan na sa da na mahaifin sa
Wani mutum mai suna Odukoya Ibraheem da ya bayyana a gaban wata kotu na garin Abeokuta don neman rabuwa da matar sa, ya kasa tuna sunan mahaifin sa da na 'ya'yan sa a yayin da kotu ta bukaci hakan.
Wani Bawan Allah ya kidime bayan ya gurfana gaban kuliya
Ibraheem mai yara mata guda 2, ya nemi kotu ta raba auren ne saboda a cewar sa, babu kauna da zaman jin dadi a auren. Ibraheem dai cike yake da tsoro yayin da alkali ke masa tambayoyi.
Abu kamar wasa, ko da a ka tambaye shi sunan mahaifin sa, sai ya daburce ya kasa fadi kai tsaye. A cewar sa tsoro ne ya mantar da shi sunan. Haka dai ya dunga inda-inda duk lokacin da a ka jefa masa tambaya, babu wata gamshasshiyar amsa da ya iya bayarwa.
Wannan al'amari ya sa mutanen da ke kotun su ka tuntsure da dariya. Daga nan ne alkalin ya yi watsi da shari'ar.
Labels: Labarai