Rahotanni sun kawo cewa wani jirgin kasa dake jiila daga tashar jirgi na garin Zariya zuwa Kauran Namoda dake jihar Zamfara yayi hatsari a karamar hukumar Funtuwa.
Jirgin ya baro Kauran Namoda inda hatsarin ya afku a daidai kwanar Goya yayinda tarago biyar na jirgin cike da mutane ya kife.
A cewar daya daga cikin wadanda abun ya cika dasu, Nafisa ta sanar da cewa jirgin na dauke ne da sama da mutane dari biyu da kuma kaya amma dai mutane uku kawai ne suka karye yayin da wasu suka ji rauni.
Mutanen da abin ya faro akan idanun su sun shedawa wa majiyarmu ta Leadership cewa garin kwana ce kuma direba ya taho babu sassauci aguje yake shi yasa Jirgin ya daɗi.
Shi kuwa Direban ya bayyana cewa Jirgin ya kwace masa ne Sanadiyar hatsarin kenan.