Ina Tawali'un Shugaba Buhari yake, ya kamata a saki El-Zakzaky - Inji wani lauya mai kare hakkin dan Adam

Fitaccen lauya mai kare hakkin dan Adam Femi Falana, ya rubuta wa shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya ke rokon sa akan ya kasance mai tawali'u ta hanyar bayar da umarnin sakin shugaban kungiyar Shi'a Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, da kuma matar malamin, Zainab, daga daurin da ake musu wanda ba bisa ka'ida ba.
Hausansi ta fahimci cewa, shugaban kungiyar ta Shi'a da mai dakin na sa suna tsare a hannun hukumar DSS tun a watan Dasumba na shekarar 2015, sakamakon arangama a garin Zaria dake jihar Kaduna, tsakanin mabiyan El-Zakzaky da tawagar shugaban hafsin sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai.
Buhari ka tausaya ka bayar da umarnin sakin El-Zakzaky - Falana
Wannan wasika da Lauyan ya rubuto a ranar 7 ga watan Nuwamba, ita ce ta biyu da ya aika fadar shugaban kasar inda yake kira akan sakin wadanda aka tsare. Wasikar farko ta zo ne tun a ranar 2 ga watan Yuni inda ya aikawa mataimakin shugaban kasa a lokacin da yake mukaddashin shugaban kasa yayin da shugaba Buhari ya fita neman lafiya a birnin Landan.
Babban lauyan wanda cikin wasikar ya tunatar da shugaban kasa cewa, ci gaba da tsare ma'auratan ya saba wa dokar babbar kotun tarayya. Ya roki shugaban kasar ya yi la'akari kan halin da suke ciki.
Babban lauyan ya tunatar da shugaba Buhari irin halin da ya shiga a lokacin da tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida ya tsare shi ba bisa ka'ida ba, saboda haka ya tausaya wa irin azabar da El-Zakzaky yake ciki shi da iyalin sa.

Labels: