IBB ya yaba wa gwamnan jihar Ribas game da kokarin sake farfado da jam’iyyar PDP
- Wike ya jagoranci wasu shugabannin jihar Ribas zuwa ziyarar tsohon shugaban kasa a gidansa da ke Hilltop a Minna
- IBB ya ce yana alfahari da gwamnan game da kyakyawar shugabancin sa
Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya yaba wa gwamnan jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, game da kokarin da yake yi wajen inganta harkokin siyasa a Najeriya.
Da yake jawabi a ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba a lokacin da gwamnan Ribas, Nyesom Ezenwo Wike ya jagoranci wasu shugabannin jihar Ribas zuwa ziyarar sa a gidansa da ke Hilltop a Minna, babban birnin jihar Neja, tsohon shugaban kasar, ya yaba wa gwamna game da kokarin farfado da jam'iyyar PDP.
Majiyar hausansi ta tabbatar da cewar, IBB ya lura cewa kasar tana buƙatar wata jam’iyyar adawa mai karfi.
Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike
Ya ce: "Shi ya sa nake yaba kokarin da gwamnan jihar Ribas ke yi don tabbatar da cewa ana yin siyasa ta hanyar da ta dace a kasar kamar yadda ake yi a kasashen duniya da suka ci gaba”.
IBB ya gode wa gwamnan game da kyakyawar shugabancin sa. Ya ce labarin nasarorin gwamna Wike sananne ce.
Da yake jawabi game da zaben Anambra, tsohon shugaban sojan Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce, an yi zaben da gaskiya. Ya ce bai yi mamakin sakamakon zaben ba, saboda an shirya wa zaben.
Ya ce: "Wannan ya nuna cewa 'yan Najeriya zasu iya gudanar da kansu a cikin zaman lafiya".
Da yake jawabi ga 'yan jarida bayan ziyarar, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, ya ce shugabannin jihar sun kasance a Minna don neman shawarar shugaban a matsayin shugabannin PDP.
Labels: Labarai