Hukumar SON ta samu nasarar kama mota cike da haramtaciyar siga akan iyakar Kebbi da kasar Benin
- Gwamnatin Najeriya ta haramta shigo da siga kasa Najeriya daga kasashen waje
A cikin kudirin gwamnati tarayya na kare yan Najeriya daga sayan kayan abinci mara sa kyau wanda zai cutar da su.
Hukumar SON ta samu nasarar kama wata babbar mota cike da buhunar haramtaciyar siga da aka shigo da shi kasar Najeriya akan Kebbi da kasar Benin.
Shugaban hukumar SON na jihar Kebbi, Jibril Muhammad ya sanar da haka ranar Litinin a lokacin da ya zanta da yan jarida a Birinin Kebbi.
Hukumar SON ta kama mota cike da Siga a iyakan Kebbi da kasar Benin
Ya ce “sun sami labarin shigowar da buhunan ne ta iyakan Kebbi, Benin da jamhuriyyar Nijar daga kasar Brazil.
Muhammad “ya ce a cikin kwanaki uku da suka fara aiki a jihar Kebbi, sun kama buhunan siga a cikin kasuwan Birinin Kebbi wanda yawan su ya kai 610.
“Buhunan sigan ‘yan kg 50 da muka kama na dauke da sunan ‘White Crystal Nardini Agro Industrial and LTD Industrial Brazillaira’ da farashin Naira 15,000 kan kowace buhun a kasuwan Birinin Kebbi wanda farashin kayan ya kai Naira miliyan 9.15.”