Harin Mubi: Mutane 50 ne zuwa yanzu suka rasa ransu

Mutane 50 sun rasa ran su a bam din da ya tashi a Mubi

- 'Yan sanda na kokarin gano wadanda suka ji rauni

- Yaro ne dan kunar bakin wake ya tada bam din a masallaci

Hukumar ‘yan sandan Adamawa ta ce mutanen da suka rasa ran su sakamakon bam din da dan kunar bakin wake ya tada sun kai 50.

Malam Usman Abubakar ma’aikaci a hukumar ya tabbatarwa da gidan jarida da faruwar hakan wanda ya shaida cewa wanda ya tada bam din yaro ne a lokacin da ake sallar asuba.

Mutane 50 ne zuwa yanzu suka rasa ransu a bam din da ya tashi a Mubi

‘An samu mutane 50 da suka rasa ran su, a yanzu haka muna kokarin duba yawan wadanda suka sami rauni’Malam Abubakar.

A safiyar yau ne ciyaman na karamar hukumar Mubi, Musa Bello ya ce an tabbatar da rasuwar mutane 22 a safiyar da aka kai harin.

Hausansi ta sami rahoton tashin bam din a unguwar Dazala da ke Mu.bi da karfe 5 na safe yayin da ake gudanar da sallar asuba a masallaci

Labels: