Shugaban Buhari ya amince da mambobin kwamitin da zai tattauna karin sabon albashi
- Ministan ya ce tsohon albashin ma’aikatan Najeriya ta gushe tun a watan Agustan bara
- Ngige ya ce za mu yi yarjejeniya ranar da kwamitin za ta zauna
Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya amince da mambobin kwamitin da aka gabatar masa domin tattauna sabon farashi mafi kyau ga ma'aikatan Najeriya.
Hausansi ta ruwaito cewa, ministan kwadago, Dokta Chris Ngige, ya bayyana wannan a cikin ganawar da manama labarai bayan ganawa da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa, Abuja.
Ministan ya ce an kafa kwamiti wanda ke da wakiltar gwamnatin tarayya da jihohi, da kuma kamfanoni masu zaman kansu.
Ya ce: " Tsohon albashin ma’aikatan Najeriya ta gushe a watan Agustan bara kuma yanzu muna kan aiwatar da sabon tsarin albashi”.
"Shugaban kasa ya amince da mambobin kwmitin kuma da zarar ma'aikatan suka dawo daga taro a Geneva, za mu yi yarjejeniya ranar da kwamitin za ta zauna da gwamnonin saboda kwamitin gwamnatin tarayya da jihohi da kuma kamfanonin: NECA, MAN, NACCIMA da kuma SMEs”, inji shi.