Nasir El-Rufai ya gode ma Reverend Josiah Idowu-Fearon, tsohon limamin Anglican na Kaduna bisa karban shugabancin hukumar wanzar da zaman lafiya na Kaduna
- Gwamnan ya kuma gode ma sauran mambobin hukumar ciki harda Priscilla Ankut, mataimakiyar shugaban hukumar wanzar da zaman lafiyan
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya kaddamar da hukumar wanzar da zaman lafiya na jihar Kaduna a kokarin kawo karshen rikici dake addabar jihar.
A lokacin kaddamarwan a ranar Alhamis, 2 ga watan Nuwamba, El-Rufai yace hukumar wanzar da zaman lafiya zai taimaka wajen dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Gwamnan ma ya gode ma Reverend Josiah Idowu-Fearon, tsohon limamin Anglican na Kaduna bisa karban shugabancin hukumar wanzar da zaman lafiya na Kaduna.
Ya kuma gode ma sauran mambobin hukumar ciki harda Priscilla Ankut, mataimakiyar shugaban hukumar wanzar da zaman lafiyan, Saleh Basayi Momale, Hajiya Khadija Hawaja Gambo bisa yarda da sukayi suyi aiki a matsayin kwamishinoni na din-din-din.
Labels: Labarai