Gwamnan Gombe ya sha alwashin samar da wata cibiyar addinin Islama a jiharsa
- Ginin zai kunshi masallacin Juma'a da Islamiyya
- Sheikh Nasiru Kabara yayi kira ga musulmai da su hada kan su
Gwamna Ibrahim Dan-Kwambo ya sha alwashin samar da wata cibiyar addini mai suna 'Al-Ihsan Islamic Centre Gombe' a jiharsa kafin watan Mayu 2019.
Ya shaida cewa za a kafa cibiyar ne don bunkasa ilimi a jihar da kasa baki daya, ya kuma bada tabbacin ne a taron Maulidi da aka yi wanda ’yan kadiriyya suka shirya a jihar.
DanKwambo zai gina cibiyar addinin Islama
Cibiyar an fara gina ta ne a kan titin Gombe-Kano, zai kunshi babban masallacin Juma’a da Islamiya don haddar Al-Kurani.
Yin hakan, gwamnan ya shaida cewa za a sami dimbin lada daga Ubangiji, don haka wasu kungiyoyin ma zasu iya tallafawa a gina cibiyar don samin lada. Tuni gwamnatin ta kafa wasu irin makarantun 11 a cikin jihar.
Mataimakin gwamnan jihar Kano da ya wakilci Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yaba da wannan aiki, ya kuma ce lallai wannan cibiya zata taimaka wajen samin ingataccen addinin Islama
Sheikh Nasiru Kabara shugaban kungiyar ‘yan kadiriyya na Afirka ya bada tabbacin cewa aikin zai bada kyakkyawan sakamako a rayuwar mutanen jihar. Sannan ya yi kira ga musulmai da su h
Labels: Labarai