Tafiyar Shugban Kasa Buhari zuwa Turkiyya tayi amfani
- Kamfanonin Kasar wajen sama da 20 sun shigo Najeriya
- Najeriya za ta amfana daga ziyarar da Shugaban ya kai
Mun samu labari cewa alheri ya fara bayyana bayan zuwan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Kasar Turkiyya kwanakin baya.
Shugaban Kasar Turkiyya tare da Shugaba Buhari da Iyalin sa
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara Kasar Turkiyya kwanakin baya inda ya bayyana cewa ziyarar za ta bunkasa harkar kasuwanci tsakanin kasashen biyu. Yanzu haka dai an fara cin gajiyar wannan tafiyar a Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa sama da Kamfanoni 23 su ka shigo Najeriya daga Kasar Turkiyya ta Turai domin harkar kasuwanci kwanan nan. Akwai kamfanoni da su ka shahara wajen harkar kayan wuta da yanzu haka su na Najeriya.
Tafiyar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi a watan jiya na Oktoba na kwanaki 4 zuwa kasar ne dai ya jawo wannan abin alheri. Alakar kasashen biyu dai ya kara karfi bayan da Shugaba Buhari ya gana da takwaran sa Tayyib Erdogan.