- Tsohon jakadan Najeriya a Kanada ya ce ficewar Atiku ta tabbatar da cewa Buhari ya kasa wa ‘yan Najeriya
- Bejide ya bayyana cewa shigowar Atiku a PDP zai taimaka wajen sake samun shugabanci a 2019
- Bejide ya ce idan kudu maso yamma ba ta samu shugabancin PDP ba, zai iya kasance babban kalubale ga jam’iyyar
Tsohon jakadan Najeriya a Kanada, Amb. Dare Bejide, ya ce ficewar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar daga jam’iyya mai mulki ta APC zuwa PDP wata alamar cewa shugaba Muhammadu Buhari ya kasa wa 'yan Najeriya.
Bejide, dan takarar gwamna jihar Ekiti a karkashin jam’iyyar PDP, ya nuna cewa yana da hatsari ga jam'iyyar APC da ta rasa wani dan siyasa irin Atiku, yana cewa, "Shigowa ga jam'iyyarmu zai taimaka mana mu sake samun shugabanci a 2019".
Game da zaben shugabancin jam'iyyar PDP, Bejide ya ce ba zai yiwa jam’iyyar kyau ba idan kudu maso yammacin kasar bai kai ga shugabncin jam’iyyar ba.
Shugaba Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar
Tsohon gwamna Gbenga Daniel da Cif Bode George da Farfesa Tunde Adeniran da kuma Jimi Agbaje sune masu neman shugabanci jam’iyyar daga yankin.
Kamar yadda Hausansi ke da labari, Bejide ya yi wannan magana ne a Ikere Ekiti a ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba a lokacin ganawar da wasu 'yan jam'iyyar a karamar hukumar gabanin zaben gwamnan jihar wanda za a gudanar a shekara ta 2018.
Labels: Labarai