- Gwamnan Ekiti Fayose ya cika shekaru 57 a Duniya
- Shugaban Kasa Buhari bai taya Gwamnan murna ba
- Wannan abu bai yi wa Gwamnan dadi ba ko kadan
Mun samu labari cewa kwanan nan kuma Gwamna Ayodele Fayose ya kara sukar Shugaban kasa Muhammadu Buhari kamar yadda ya saba.
Ko yaushe Gwamna Fayose zai rabu da Shugaba Buhari
Wannan karo Gwamnan ya soki Shugaban Kasar ne a dalilin rashin taya sa murnar zagayowar ranar haihuwar sa. A jiya Laraba ne Gwamna Ayo Fayose ya cika shekaru 57 da haihuwa a Duniya a babban birnin Ekiti na Ado-Ekiti.
Fayose ya koka da cewa Shugaban Kasar bai tanka da shi ba a wannan ranar farin ciki ganin cewa yana cikin Gwamnoni kuma manyan ‘yan adawa a Kasar. Fayose yace shi fa ba makiyin Shugaban Kasa Buhari bane iyakar ta adawa ce kurum.
Gwamna Fayose ya dade yana sukar Shugaban Kasar amma yace wannan shi zai sa Shugaban Kasar ya gyara rawar sa. Kwanan nan ya soki Shugaba Buhari bayan da ya goyi bayan sallamar Malaman Makarantar da Gwamnatin Kaduna za tayi.
Labels: Labarai