El-Rufai ya bayyana hanyoyi 5 da bashin dala miliyan 350 zai amfani jihar Kaduna

Haryanzu dai ba’a gama sa-toka sa-satsin daya dabaibaye batun ciyo bashin dala miliyan 350 da gwamnatin jihar Kaduna ta nemi ta ciyo daga bankin Duniya ba.
Tasgaron da gwamnatin jihar ke fama da shi kuwa shine rashin amincewa da ranto kudaden da kwamitin sa ido akan ciyo basussuka na majalisar dattawa karkashin shugabancin Sanata Shehu Sani tayi.

Sai dai jaridar Premium Times ta ruwaito gwamnan ya shaida ire iren abubuwan da zai yi da kudaden, da zarar sun shigo hannunsa, inda yace duk abin da zai yi da kudin ba zai wuce ayyukan da yayi ma jihar Kaduna alkawarin yi ba.
Wasu daga cikin ayyukan kamar yadda majiyar Hausansi ta ruwaito su sun hada da:
1- Samar Kayan aiki a Makarantu
El-Rufai ya bayyana cewa wani kaso daga cikin kudin zai tafi kacokan wajen samar da ingatattun kayayyakin aiki a makarantun gwmnati da zasu taimaka wajen samar da yanayi mai kyau na koyarwa da karatu. Daga cikin kayan akwai Kujeru, Tebura, Kofofi, Taga, bayika,ruwan sha, lantarki da kwanukan rufi.
2- Gina sabbin makarantu/Ajujuwa
Gwamnan yace daga cikin manufarsu ta amso wadannan kudade akwai batun sake gina sabbin ajujuwa da ma makarantu, inda yace saboda ajujuwan dake da akwai yanzu basa iya daukan karin daliban da aka samu a makarantun jihar.
3- Gyaran Asibitoci
A cigaba da zayyana ayyukan da gwamnatin jihar Kaduna zata yi da bashin dala miliyan 350, gwamnan yace zasu samar da kayan aiki a manyan asibitocin jihar guda 25 da kuma kanana guda 225.
4- Hanyoyi
Ga wadanda suka san jihar Kaduna, sun san tuni an fara ayyukan hanyoyi daban daban, da suka hada da sabunta tsofaffin hanyoyi da kuma gina sababbi, don haka ne gwamnan yace za’a kashe kaso mai tsoka na kudin don wannan aikace aikace.
5- Ruwan Zaria
El-Rufai ya bayyana karasa aikin ruwan Zaria da gwamnatinsa ta tarar ana yi a jihar, wanda ya kwashe shekaru da dama, daga cikin abubuwan da zai yi da kudaden, tare da fadada ruwan sha na famfo ga sassan jihar.

Labels: