EFCC ta gano gwamnoni 3 da suka karkatar da kudaden Paris Club da aka ba su dan biyan albashin ma'aikatan jihohin su
- Hukumar EFCC ta yi alkwarin gurfanar da duka mutane da ta ke zargi karkatar da kudaden Paris Club
Wani jami'in hukumar EFCC ya fada wa yan jarida cewa suna tuhumar gwamnoni 3 da laifin karkatar da Kudin Paris Club da aka raba mu su dan biyan albashi ma’aikatan jihohin su.
Wannan kari ne ga gwamnoni 2 da EFCC ta ke zargin su da karkatar da kudaden Paris Club a kwanakin baya.
Wani jami’in EFCC ya bayyana cewa sun gano wata asusun ajiyan banki malakar shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya da aka karkatar da kudaden Paris Club.

EFCC ta bayyana dalilin da ya sa wasu jihohi basa iya biya albashi
Hukumar EFCC ta gano kudaden da aka karkatar zuwa asusun ajiyan banki na wasu tsirarrun mutane, da sunan biyan albashin kwararrun masu ba da shawara (Consultancy Fee).
"Wannan shine dalilin da yasa har yanzu wasu jihohi ba sa iya biyan albashi. “Nan gaba zamu fitar da cikakkyar jawabi ga al’ummar akan abubuwan dake faruwa.
"Kuma munyi alkwari gurfanar da duka wadanda muke zargi.
“A yanzu haka mun rubuta wa kotu ta ba mu umarni kwace naira biliyan N1.823 da shugaban gwamnonin Najeriya ya biya wasu kwararrun masu ba da shawara a matsayin albasin su,"Inji jami'in EFCC.