Duk Wanda Ya Kara Ce Mun jahila Allah Ya Isa - Jaruma Ummah Shehu

Fitacciyar jarumar nan ta wasanHausa a masana'antar Kannywooddin nan mai suna Ummah Shehu ta mai da kakkausan martani ga masusukar ta da ce mata jahila inda ta bayyana cewa dukkan wanda ya kara furta wannan kalmar a kanta, to ba ta yafe masa ba kuma ta barsa da Allah.
Jarumar wadda a kwanan baya dai labarin ta ya dabaibaye kafafen sadarwar zamani inda aka zargeta da karancin ilimin addinin Islama biyo bayan wata fira da tayi a gidan Talabijin na Arewa 24 inda ta kasa fadin sunan wadda ta reni manzon tsira Annabin Rahma SAW.
Hausansi ta samu dai cewa a cikin wata fira da jarumar tayi a kwanan baya, ta bayyana cewa ita fa duk a cikin raha ma ne da dariya aka yi mata tambayar kuma ba don bata sani bane ba ta bada ansar sai dai kawai don ta ga ba hurumin ta bane.
Jarumar ta kuma kara da cewa ita tasan tana da kwarewa dai-dai gwargwado ta wannan fannin domin hakan ne ma ya sa ta shigo harkar fim don ta bada gudummuwar ta.


Labels: